An garkame shaguna fiye da 280 da ake saida magunguna a Zamfara

An garkame shaguna fiye da 280 da ake saida magunguna a Zamfara

- Majalisar kula da harkokin magunguna tayi wani babban aiki a Jihar Zamfara

- An rufe shaguna sama da 200 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a fadin Jihar inji PCN

- Wasu na saida magungunan da ba su da lasisi yayin da wasu ke abin da su ka so

Mun samu labari a Lahadi jiya cewa Majalisar PCN ta masu kula da harkokin magunguna sun rufe shaguna da dama da ake saida magunguna a Jihar Zamfara saboda sabawa ka’idojin aiki.

Shaguna akalla 280 aka rufe a Jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya inji wata Darekta ta PCN Anthonia Aruya. Aruya ta bayyana wannan ne a cikin Garin Gusau inda tace ya zama dole su dauki wannan mataki domin kare rayukan jama’a.

KU KARANTA: Wasu 'Yan Kungiyar asiri sun yi karen-batta a Najeriya

Darektar ta PCN tace wasu marasa lafiya na dirkar guba ne da sunan magunguna ba su sani ba saboda rashin tsabta da kula a dakunan saida maganin. Wasu dakunan saida magungunan ma dai su na aiki ba tare da akwai wanda ya san aikin ba.

Har wa yau babbar Jami’ar ta PCN tace shaguna da dama ba su da rajista don haka babu wanda ya san irin danyen aikin da su ke yi. Duk shagon da bai da rajista dai yana iya saida magungunan da ba a san da zaman su ba kuma jama’a su cutu.

PCN dai tace za ta cigaba da yin aikin ta a Kasar gaba daya domin tsabtace harkar saida maguguna. An kuma yi kira ga jama’a su tabbatar cewa an yi wa magani rajista kafin su saya a shago.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel