A-cigaba-da-gashi: Jam'iyyar APC ta maye gurbin Sakataren taron gangamin ta da yayi murabus
Jam'iyyar mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) a jiya ta sanar da nada sabon Sakataren kwamitin taron gangamin ta watau National Convention Committee (NCC) biyo bayan murabus din da Sanata Benjamin Uwajumogu yayi a jiya.
Wanda zai maye gurbin sa, kamar dai yadda muka samu shine Sanata Victor Ndoma-Egba. Wannan dai na kunshe ne a cikin wani sakon kar-ta-kwana da jami'ain hulda da jama'a na jam'iyyar ta APC Malam Bolaji Abdullahi ya fitar a shafin sa na Tuwita.
KU KARANTA: Shekaru 4 sun yi wa duk mai son kawo gyara a Najeriya kadan - Osinbajo
Legit.ng ta samu cewa ana kishin-kishin din dai cewa tsohon Sakataren na kwamitin yayi murabus ne daga mukamin sa sakamakon matsin lamba daga gwamnan jihar sa ta Imo wanda yayi barazanar ficewa daga jam'iyyar idan har bai yi murabus din ba.
A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party, PDP ta samu nasarar lashe zaben cike gurbi na dan majalisar jiha da ya gudana a jihar Oyo dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya na mazabar Ibarapa ta gabas.
Mukamin dai idan mai karatu bai manta ya samu ne biyo bayan mutuwar wanda yake rike da kujerar Michael Adeyemo da ya kasance kakakin majalisar jihar kafin mutuwar sa a watannin baya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng