Wasu ‘Yan fashi da aka kama sun ambaci sunan Bukola Saraki a matsayin Mai gidan su
Yanzu nan mu ka samu labari cewa Jami'an 'Yan Sandan Najeriya sun gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya hallara a gaban su kan wani fashi da aka yi kwanaki a Jihar Kwara domin ya wanke sa.
Idan ba ku manta ba dai kwanaki ne aka yi wani mummunan fashi da makami a wani banki a Garin Offa da ke cikin Jihar Kwara. Ana zargin cewa akwai sa hannun Shugaban Majalisar Tarayyan a wajen wannan danyen aiki.
Yanzu haka Rundunar ‘Yan Sandan kasar ta aikawa Bukola Saraki gayyata domin ya amsa wasu tambayoyi game da fashin da aka yi. An samu mutum 5 cikin wadanda ake zargi da laifin fashin sun ambaci sunan Bukola Saraki.
Mutum 15 da ake tunanin da su aka yi wannan fashi sun shiga hannun Jami’an tsaro. Ana zargin cewa wasun su su na yi wa Bukola Saraki aiki tun lokacin yana Gwamnan Jihar Kwara. A 2007 ne Saraki ya bar Gwamna ya zama Sanata.
KU KARANTA: Ana tsananin fama da duhu a Garin Shugaban Kasa Buhari
An dai kashe mutane sama da 30 lokacin da aka yi wannan fashi daga ciki har da wasu mata masu juna-biyu. Daya daga cikin ‘Yan fashin yace ba Bukola Saraki ya tura su wannan aiki ba amma dai tabbas ya san da zaman su.
Daga cikin kayan da ‘Yan Sandan su ka samu wajen wadannan mutane da ake zargi har da wata mota da Bukola Saraki ya taba ba wani kyauta. Kwanaki dai Saraki yace Sufetan ‘Yan Sanda na kokarin jefa sa cikin wani mugun kulli.
Dazu kun ji cewa ‘Yan Sanda sun damke Sojojin gona 3 a Jihar Osun da ke garkuwa da mutane. Sunan wadanda aka kama dai Henry Omenihu, Paul Chituru, da kuma Henry Bright.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng