Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wasu masu garkuwa da mutane a Jihar Osun
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Osun Fimihan Adeoye ya bayyana cewa an kama wasu mutane 3 a Garin Osugbo bayan sun sace wasu Bayin Allah sun yi garkuwa da su kwanakin baya.
Fimihan Adeoye wanda shi ne Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ke fadawa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun harbi motar da wani Kayode Agbeyangi da Oyeyemi Obafemi su ke ciki wanda hakan ya sa tayar su ta sace.
Bayan tayar a fashe ne dole wadannan Mutane su ka ci burki domin su yi gyara, a nan ne wadanda ake zargin su ka zo su kayi gaba da su. Wadanda ake zargin sun zo ne sanye da kayan Sojoji su ka yi ram da su zuwa wani Daji inda su ka tsare su.
KU KARANTA: Gwamnatin Borno ta rusa gidajen karuwai da giya
Jami’in ‘Yan Sandan yake cewa sai da ‘Yan uwan wannan mutane su ka biya kudi har Naira Miliyan 2 sannan aka sake su. Wannan karo ne dai Allah yayi dubun su ta cika kuma za a maka su gaban Kotu domin ayi shari’a inji Hukumar 'Yan Sanda.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, sunan wadannan mutane da ake zargi Henry Omenihu, Paul Chituru, da kuma Henry Bright. Su kan dai yi basaja ne da kayan Sojoji kamar wasu Jami’an tsaro dauke da manyan makamai da harsashi iri-iri.
Kwanaki kun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni a dauki sababbin Jami’an ‘Yan Sanda 6000. A hawan wannan Gwamnatin an dai dauki Ma’aikata 10000 na ‘Yan Sanda domin inganta tsaro a kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng