PDP ta ba Jam’iyyar APC mamaki a zaben Majalisar Dokoki

PDP ta ba Jam’iyyar APC mamaki a zaben Majalisar Dokoki

- An tika Jam’iyyar APC da kasa a wani zabe da aka yi a Jihar Oyo

- Wani Matasahi daga PDP ne ya doke APC a zaben Majalisar dokoki

- An yi zaben ne domin maye gurbin ‘Dan Majalisar Mazabar Ibarapa

Jiya ne mu ka ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kashi a wani zabe da aka yi na Majalisar dokoki a Jihar Oyo. Abin mamaki dai shi ne ana tunani Jam’iyyar APC mai mulki ce ke da karfi a Jihar.

Honarabul Adebo Ogundoyin ne ya lashe zaben kujerar ‘Dan Majalisar dokokin Yankin Gabashin Garin Ibarapa da ke cikin Jihar Oyo. Jam’iyyar PDP ta taya ‘Dan takarar na ta murnar lashe wannan kujera a zaben da aka yi.

Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya taya matashin ‘Dan takarar murnar samun nasarar cin wannan kujera ta Majalisar Jihar. Adebo Ogundoyin dai Matashi ne mai shekaru 30-da-wani-abu kuma yana da Digiri.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban Hukumar ICPC na kasa ya rasu

An yi zaben ne domin maye gurbin Kakakin Majalisar dokokin Jihar wanda ya rasu kwanakin baya. Kamar yadda mu ka samu labari ‘Dan takarar na Jam’iyyar adawa Adebo Ogundoyin yayi karatu ne a Jami’ar nan ta Babcock.

Wanda yayi nasara 'Dan uwan Kakakin Majalisar Jihar da ya rasu ne kwanaki watau Marigayi Micheal Apeyamo wanda ya cika yana da shekaru 47. Jami'in zaben Ayodeji Omole ya sanar da cewa Ogundoyin polled ya samu kuri'a 6277.

'Dan takara APC a zaben Olukunle Adeyemo ya zo na biyu ne inda ya tashi da kuri'a 4,619 kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.

Kwanaki kun ji cewa wasu manyan Jam’iyyar APC sun koka da abin da ya faru wajen zaben shugabannin Jam’iyyar da aka yi kwanaki a Jihar ta Oyo. PDP kuma dai ta dage cewa dama za ta ba Matasa dama a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel