Wani uba ya kashe diyar sa a jajiberin auren ta
Wani mutum mai shekaru 60 a duniya, Mista Cletus Agulaka ya kashe diyar sa Miss Onyinye Agulaka ta hanyar sarar ta da adda a yayin da ta ke sharar barci.
Rahottani sun bayyana cewa yau Asabar 2 ga watan Yuni ne ya kamata ayi bikin daurin auren diyar a kauyensu kamar yadda Punch ta ruwaito.
Lamarin dai ya afku ne misalin karfe 2 na daren Juma'a a kauyen Osikwu Awgu da ke karamar hukumar Otumba North na jihar Anambra.
KU KARANTA: Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda
A cewar mahaifiyar diyar, Mrs. Georgina Agulaka, rikici ya barke ne a yayinda Cletus ya dawo gida a daren Juma'ar bayan ya yi tatil da giya ya fara nemar torch light dinsa amma bai gani ba.
"Yaransa sun fada masa cewa basu san inda ya ajiye torch light dinsa ba sai ya yi biris da zancen kamar ya huce, amma kwatsam sai ya farka misalin karfe 1 na dare ya dauke da adda kuma ya sari diyarsa," inji Mrs Agulaka
Wani ganau ya ce mahaifin ya fice ta taga kuma ya cika wandon sa da iska yayin da ya hangi 'yan bangan kauyan sun nufo gidansa inda daga baya suka tafi da gawar diyar zuwa asibiti.
Kakakin hukumar Yan sandan jihar, Mista Haruna Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin yayinda ya ke zantawa da manema labarai a garin Awka.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 31 ga watan Mayun misalin karfe 2 na dare kuma wanda ake tuhumar ya shigo hannun hukuma a jiya 1 ga watan Yuni.
"A halin yanzu ana cigaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar dashi a kotu," inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng