Gwamnati ta ceto kusan Tiriliyan daya daga masu mugun taurin bashi a kasar nan
- Shugaban jami'an AMCON, Mista Ahmed Kuru ya bayyana hakan a wata tataunawa da 'yan jaridu jiya a Legas
- Kuru yace kungiyar ta mallaki anguwanni dauke da gidaje da yawa da sauran ire iren kadadori
- AMCON ke da alhakin kare dukiyoyi a harkar hada-hada
Asset Management Crporation of Nigeria (AMCON) ta lissafa kudin bashin da aka biya a karshen 2017 a Naira biliyan 740. Wannan kawai sakamakon kungiyar ne a 2017 wanda ya nuna faduwar matsayin ta ya ragu da kashi 90 cikin dari zuwa Naira biliyan 164.94 wanda aka lissafa a shekarar da ta gabata.
Shugaban jami'an AMCON, Mista Ahmed Kuru ya bayyana hakan a wata tataunawa da 'yan jaridu jiya a Legas.
Kuru yace kungiyar ta mallaki anguwanni dauke da gidaje da yawa da sauran ire iren kadadori.
Yace: mun rabu da wasu kadarorin kudi wanda suka hada da bankuna guda uku. Muna so mu siyar da kamfanin pijo na najeriya.
"Wannan kari ne ga kananan kasuwanci da muka rabu da wasu, wasu kuma muka rabu dasu."
Ya misalta kudin da AMCON ta tallafawa bangaren noma da kiwo da Naira tiriliyan 1.7.
"A tsarin AMCON da farko shine, da farko ana zaton wadannan basussukan za a gyara tsarin su da darajar su"
DUBA WANNAN: Dalilan da suka sa aka qi rage shekarun zama gwamna da sanata- majalisa
"Amma kuma, da yawan kasuwancin da aka gyara musu tsarin su kuma aka basu kudi a baya, yanayin tafiyar kasuwancin ba abin dogaro bace."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng