Babban bankin Najeriya CBN ya sake antayo dala kasuwannin canji don tsare Naira daga durkushe wa

Babban bankin Najeriya CBN ya sake antayo dala kasuwannin canji don tsare Naira daga durkushe wa

- Har yanzu farashin Naira na tambal-tambal

- A da CBN ta hana dalar, abin da ya jawo kacimemeniya a kasuwar canji

- Yanzu kam dalar na samuwa a kan kari, don haka naira ta dan tsaya da kafarta

Babban bankin Najeriya CBN ya sake antayo dala kasuwannin canji don tsare Naira daga durkushe wa
Babban bankin Najeriya CBN ya sake antayo dala kasuwannin canji don tsare Naira daga durkushe wa

A kokarin gwamnatin Tarayya na daidaita farashin naira da dala a kasuwannin canji na banki da na gwamnati, da ma na 'yan kasuwa, babban bankin Najeriya CBN, ya sayar da akalla dala $331.41 million ga bankuna da 'yan kasuwa domin masu bukatar kudin na Amurka.

Sayar da dalar, yakan rage pressure da ke taruwa wajen neman kudaden kasashen waje da 'yan kasuwa da masu tafiye-tafiye kan yi da ma 'yan makarantar kasashen waje.

A yanzu farashin nairar, yana tambal-tambal ne tsakanin 364-365 ga kowace dala a kasuwar bayan fage, su kuwa bankuna suna sayar da dalar a farsshin da baya wuce 315 ga kowacce naira.

DUBA WANNAN: Buhari yace yana tsoron kudin da aka tara don kada shi daga mulki

Naira dai, ta gamu da gamonta ne tun bayan da farashin mai ya fadi warwas a duniya, Amurka kuma ta daina sayen man mu don tsoron yadda mayakan Neja Delta na iya hana a sha man gabanin zaben 2015, wanda hakan ya jawo nairas ta kai har 500.

A baya dai dala bata taba kai karfin naira ba a zamunnan 1914-180s.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel