Yanzu Yanzu: Wata ta fadi ta mutu a yayin tantance ma’aikatan da hukumar yan sanda ta diba a Abuja

Yanzu Yanzu: Wata ta fadi ta mutu a yayin tantance ma’aikatan da hukumar yan sanda ta diba a Abuja

Christiana Danjuma, wata matashiya da ta samu aikin yan sanda ta fadi ta mutu a ranarJuma’a, 1 ga watan Yuni a Abuja yayinda ake tantance lafiyar wadanda aka dauka aiki.

Matashiyar wacce ta kasance yar asalin jihar Kaduna ta fadi ta mutu ne a yayinda take cike takardan gwajin lafiyar da za’ayi masu.

Punch ta rahoto cewa anyi gaggawan kai ta babban asibitin Abuja wato National Hospital inda aka tabbatar da mutuwar ta da misalin karfe 11 na safe.

Yanzu Yanzu: Wata ta fadi ta mutu a yayin tantacce ma’aikatan da hukumar yan sanda ta diba a Abuja
Yanzu Yanzu: Wata ta fadi ta mutu a yayin tantacce ma’aikatan da hukumar yan sanda ta diba a Abuja

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar yan sandan Najeriya ta yi gayyaci mutanen da suka yi nasarar cin jarabawar daukar aiki da ta gudanar a ranar Juma’a da su zo a duba lafiyarsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An harbi tsohon dan majalisa, Opeyemi Bamidele a Ekiti

Bisa ga sunayen da aka wallafa a shafin yanar gizon rundunar yan sandan, https://psc.org.ng/candidateslist/, an umurci wadanda suka yi nasara da su je a tattance su a hedkwatan hukumar yan sanda na jihohinsu tsakanin ranar 31 ga watan Mayu da 3 ga watan Yuni.

Daga cikin mutane 37,000 da suka rubuta jarrabawar, 5, 107 suka yi nasarar shiga jerin wadanda za’a tattance a hukumar lafiyar kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku bi shafukanmu domin samun labarai https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga hanyar mallakar sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng