'Yan Najeriya 186 sun dawo daga Kasar Libya

'Yan Najeriya 186 sun dawo daga Kasar Libya

Cibiyar kula da 'yan Hijira da baƙin haure ta duniya da kungiyar hadin kan kasashen Turai watau EU (European Union), sun sake yakito wani kaso na al'ummar Najeriya daga Kasar Libya.

Kakakin cibiyar bayar da agajin gaggawa reshen Kudu maso Yamma na Najeriya, Mitsa Ibrahim Farinloye, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.

'Yan Najeriya 186 sun dawo daga Kasar Libya
'Yan Najeriya 186 sun dawo daga Kasar Libya

Mista Farinloye a ranar Juma'a ta yau ya bayyana cewa, cibiyar hijira ta duniya watau IOM (International Organisation for Migration) ta sake yakito 'yan Najeriya 186 daga Kasar Libya da suka yi ƙaura domin cirani.

KARANTA KUMA: An dakatar da ni a Majalisa yayin da na faɗi irin abin da Jega ya faɗa - Yerima

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, baƙin hauren har kaso biyu sun sauka a farfajiyar jirgin sama ta Murtala Muhammad dake jihar Legas a ranakun Laraba da kuma Alhamis din da suka gabata.

A cewar Mista Farinloye, baƙin hauren sun hadar da Mata 99, Maza 75, Yara 4 da kuma na goye guda takwas.

Ya kara da cewa, wannan sabbin kaso na baƙin haure daga Kasar Libya sun dawo Kasar su ne bisa ga ra'ayin su a yayin da cibiyar ta IOM ta basu dama ta tallafin jigilar su zuwa Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel