Jirgin sama yayi saukan bazata sakamakon warin jikin wani fasinja da ya sa sauran mutane amai da suma

Jirgin sama yayi saukan bazata sakamakon warin jikin wani fasinja da ya sa sauran mutane amai da suma

Wani jirgin sama yayi saukan bazata bayan warin jikin wani fasinja ya sanya sauran mutane dake kewaye da shi amai da suma.

Jirgin na Transavia na hanyar zuwa hutu Spain ya yi saukan bazata lokacin da matafiya suka rasa sukuni sakamakon warin jikin wani mutumi dake tashi kamar ya shafe tsawon lokaci batare da wanka ba.

Mutumin na wari sosai ta yadda ya kai har fasinjoji sun fara suma da amai bayan jirgin ya tashi daga filin jirgi na Schiphol dake Netherlands.

Jirgin sama yayi saukan bazata sakamakon warin jikin wani fasinja da ya sa sauran mutane amai da suma
Jirgin sama yayi saukan bazata sakamakon warin jikin wani fasinja da ya sa sauran mutane amai da suma

Ma’aikatan jirgin sunyi kokarin kebe shi a wani bandakin jirgin kafin matukin ya karkatar da jirgin bisa tilas.

KU KARANTA KUMA: 2019: EFCC ta bukaci bankuna da su gabatar da sunayen barayi

Sun sauka domin a fitar da mutumin dake warin daga cikin jirgin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng