An ci an sha yayin da Buhari ya karbi bakoncin Dangote da hamshakan yan kasuwa a Villa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya ma hamshakin dan attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, tare da sauran hamshakan yan kasuwan Najeriya liyafar shan ruwa a fadar Aso Rock dake babban birnin tarayya Abuja.
Legit.ng ta ruwaito an yi wannan liyafa ne a daren Alhamis, 31 ga watan Mayu, wanda baya ga yan kasuwa, wasu shugabannin jam’iyyun siyasar Najeriya ma sun samu damar halarta.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kama Tireloli makare da alburusai 300,000 da ta nufo Najeriya
A yayin wannan liyafa, shugaba Buhari ya bayyana godiyarsa da jin dadinsa da yadda yan kasuwan Najeriya, musamman Aliko Dangote suke baiwa gwamnatin goyon baya akan abubuwan da sanya a gaba, musamman harkar noma.
Daga cikin wadanda suka samu halartar taron akwai shugaban kamfanin Sahara Energy, Tope Shonubi,shugaban ma’ikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, mataimakin shugaban jam’iyar APC Sanata Shuaibu Lawan, mace mai kamar Maza, Hajiya Naja’atu Muhammad da sauransu.
A wani labarin kuma, Aliko Dangote ya baiwa rundunar Yansandan Najeriya kyautar motocin sintiri guda 150 don inganta ayyukansu, musamman a kokarinsu na yaki da miyagun ayyuka a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng