Na-kusa da Shugaba Buhari ya bayyana yadda ya sha da kyar lokacin Abacha

Na-kusa da Shugaba Buhari ya bayyana yadda ya sha da kyar lokacin Abacha

Mai ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa watau Sanata Babafemi Ojudu ya bayyana yadda tsohon Shugaban Kasa Marigayi Janar Sani Abacha ya nemi ya ga bayan sa.

Tsohon Sanatan Kasar Babafemi Ojudu wanda ya ke tare da Shugaba Buhari yanzu ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Kasa a lokacin mulkin Soja Oladipo Diya ya cece sa lokacin da Janar Sani Abacha ya nemi a kashe shi.

Na-kusa da Shugaba Buhari ya bayyana yadda ya sha da kyar lokacin Abacha
Babafemi Ojudu yace Diya ya hana a kashe shi lokacin Abacha

Mai ba Shugaban Kasar shawara yayi wani bayani wajen wani taro da aka shirya domin tubawa tsohon ‘Dan Jaridar Kasar Kunle Ajibade a Legas. Ojudu yana cikin wadanda su kayi fito-na-fito da Gwamnatin Sojan Janar Sani Abacha.

KU KARANTA: Lauyan da ake ji da shi a Duniya yace ana neman komawa mulkin Soja a Gwamnatin Buhari

A lokacin Sani Abacha yana shugaban Kasa, Babafemi Ojudu yana aikin jarida kuma yana kan gaba-gaba wajen sukar Gwamnatin sa. Abokan aikin Ojudu dai dole su ka tsere su ka bar Kasar lokacin da mutanen Abacha su ka taso su gaba.

Tsohon ‘Dan Jaridar yace ya taba yin wani rubutu a kan Gwamnatin Abacha wanda jim kadan bayan dawowan sa Kasar Janar Oladipo Diya ya aiko masa wasika cewa yayi maza ya bar Kasan don kuwa Janar Abacha ya shirya kashe sa.

Femi Ojudu ya bar Najeriya ne ya tsere zuwa Kasar Ghana daga nan ya wuce Kenya lokacin da aka nemi a kashe sa. Janar Sani Abacha ya mulki kasar ne daga 1993 zuwa 1999. Shugaba Buhari dai yayi aiki a Gwamnatin Shugaban Kasa Abacha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel