Babu abin da na ke sha’awa kamar in ga ina taimakon marasa karfi - Dangote

Babu abin da na ke sha’awa kamar in ga ina taimakon marasa karfi - Dangote

- Alhaji Aliko Dangote yace burin sa shi ne ya ga ya taimaki mai karamin karfi

- Mai kudin yace so ya ke yi ace duk Nahiyar nan babu wanda ya kai shi kyauta

- Jiya ne Gidauniyar Dangote ta rabawa Mata 13, 000 kudi domin su fara sana’a

Attajirin Kasar Afrika gaba daya watau Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa burin sa shi ne ace duk Nahiyar nan ta bakaken fata babu wanda ya kai sa yawan kyauta da alheri.

Shugaban Kamfanin na Dangote da yake jawabi jiya a Jihar Nasarawa jiya inda ya ba Mata 13, 000 jari yace ba burin sa kurum ace ya fi kowa kudi ba ne, Dangote zai so ace duk Afrika babu wanda yake taimakon Talakawa irin sa.

KU KARANTA: Maganar rusa gidan karuwai ta tada kura a Borno

Aliko Dangote ya rabawa mata a Garin Lafia kudin da ya kai Naira Miliyan 130 domin su kama abin yi. Dangote yace zai cigaba da batar da kudi na sa ne wajen ganin ya gyara rayuwar Talakawan da su ka shiga wani hali a Kasar.

Alhaji Dangote ya maida hankali ne kan samar da ilmin zamani da lafiya da abinci mai lafiya da kuma samawa marasa hali sana’a domin su rike kan su. Gidauniyar ta rabawa Mata 13, 000 kudi har N10, 000 domin su fara kasuwanci.

Hamshakin ‘Dan kasuwar dai ya kafa gidauniyar nan ta sa da ke taimakon jama’a ne tun a 1993. Dangote yace babban burin sa ne ya ga rayuwar al’ummar gida Najeriya da ma Afrika sun amfana kwari da gaske daga wannan shirin na sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel