Kisan dan Achaba: Matasa sun kai farmaki ga ofishin Yansanda, sun babbaka Motoci

Kisan dan Achaba: Matasa sun kai farmaki ga ofishin Yansanda, sun babbaka Motoci

Hankalin al’umma mazauna unguwar Ibeshe dake yankin Ikorodu na jihar Legas ya fi ana barawo tashi biyo bayan wata tarzoma da ta barke inda aka yi arangama a tsakanin Yansanda da fusatattun matasa sakamakon kisan wani dan Achaba da Yansanda suka yi.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu, inda wani dan Achaba mai suna Paul Baba Ezine ya rasa ransa sakamakon wani hatsari da ya auku a lokacin da ya yi kokarin kauce ma shingen binciken Yansanda, wanda matasan ke zargin Yansanda ne suka janyo musabbabin faruwar hatsarin.

KU KARANTA: Duk mai hankali ya san akwai bukatar mu canja canji a jihar Kano - Kwankwaso

Shaidar gani da ido ta bayyana ma majiyar Legit.ng cewa: “Dan Achabar ya goyo fasinja ne a lokacin da ya cimma wani shingen binciken Yansanda, sai yayi kokarin kauce ma shingen, kwatsam sia cikin kwata, sai kuma Yansanda suka yi biris da shi, suka dauke babur dinsa.

Kisan dan Achaba: Matasa sun kai farmaki ga ofishin Yansanda, sun babbaka Motoci
Yansanda

“Daga bisani abokan aikinsa ne suka garzaya da shi zuwa Asibiti, amma rai yayi halinsa a ranar Laraba, daga nan sai suka dauki gawarsa zuwa fadar sarkin garin, sa’annan suka garzaya da shi zuwa ofishin Yansanda dake yankin, da kyar Yansanda suka fatattakesu da harbin iska, a yayin da suke tserewa ne suka gamu da wata motar Yansanda, wanda suka babbakata, sa’annan suka yi ma direbanta dan banzan duka.” Inji majiyar.

Tun bayan faruwar lamarin, rundunar Yansandan jihar Legas ta kaddamar da samame, inda a yanzu haka ta kama miutane 63 da take zargi da hannu cikin lamarin, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan jihar, SP Chike Obi ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: