Alkali ya dage shari’ar tsohon Gwamnan Katsina da Hukumar EFCC

Alkali ya dage shari’ar tsohon Gwamnan Katsina da Hukumar EFCC

- Ana ta faman shari’a tsakanin Hukumar EFCC da tsohon Gwamnan Katsina

- EFCC na zargin Shema da sace wasu kudin Kananan Hukumomi Biliyan 11

- Lauyan tsohon Gwamnan dai ya nemi a ba su lokaci su duba takardun EFCC

Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa babban Kotun Tarayya da ke Katsina ta dage shari’ar da ake yi tsakanin tsohon Gwamnan na Katsina Ibrahim Shehu Shema da kuma Hukumar EFCC zuwa watan gobe.

Alkali ya dage shari’ar tsohon Gwamnan Katsina da Hukumar EFCC
Kotu ta dage shari'ar tsohon Gwamnan Katsina zuwa wani watan

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon-kasa na zargin tsohon Gwamnan da wani Kwamishinan sa da wani babban Ma’aikacin Hukumar ALGON ne da laifin satar kudin kananan Hukumomi wanda ya haura Naira Biliyan 11.

Lauyan tsohon Gwamna Shema ne ya nemi a dage shari’ar kuma Alkalin ya amince da hakan. Yanzu dai an kara makonni 2 domin wanda ake tuhuma ya duba zargin a ke kan sa. Alhaji Lawal Rufai da Lawal Dankaba su na cikin wadanda ake kara a Kotu.

KU KARANTA: EFCC: Za a zauna a Kotu da tsohon Gwamnan PDP a Birnin Tarayya Abuja

Babban Lauyan da ke kare tsohon Gwamnan watau Joseph Daudu SAN ya nemi a ba su lokaci su duba shaidar da Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon-kasa ta mikawa Kotu a tsanake domin kare wanda ake zargi a gaban Alkali.

Shi dai Lauyan EFCC watau Olatoke Olukayode SAN bai so aka dage shari’ar ba don kuwa takardun sun dade a hannun wanda ake zargi a cewar sa. Lauyan na EFCC yace takardun ba wani kayan gabas bane da za a dauki lokaci ana duba su.

Shi dai Alkali mai shari’a Ibrahim Maikata Bako ya dage karar har sai nan da tsakiyar watan Yuni. Kafin nan dai dama kun ji cewa ana zargin tsohon Gwamnan na PDP da laifin yin awon-gaba da kudin SURE-P.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel