Shakira taki amsa gayyatar kasar Isra'ila, sannan tayi Allah wadai da kisan gillar da suke yiwa Falasdinawa

Shakira taki amsa gayyatar kasar Isra'ila, sannan tayi Allah wadai da kisan gillar da suke yiwa Falasdinawa

Fitacciyar mawakiyar nan ta kasar Colombia wacce aka fi sani da Shakira ta watsawa Yahudawan kasar Isra'ila kasa a ido, inda ta nuna goyon bayan ta dari bisa dari ga Falasdinawa

Mawakiyar tace ita bata goyon bayan mutanen da basu san darajar ran dan adam ba, saboda haka ta fasa shirya shagalin data yi niyyar hadawa a birnin Tal Aviv

Shakira taki amsa gayyatar kasar Isra'ila, sannan tayi Allah wadai da kisan gillar da suke yiwa Falasdinawa
Shakira taki amsa gayyatar kasar Isra'ila, sannan tayi Allah wadai da kisan gillar da suke yiwa Falasdinawa

Fitacciyar mawakiyar nan ta kasar Colombia wacce aka fi sani da Shakira ta watsawa Yahudawan kasar Isra'ila kasa a ido, inda ta nuna goyon bayan ta dari bisa dari ga Falasdinawa. Mawakiyar ta fasa yin shagalin wasan da aka gayyace ta tayi a Tel Aviv, babban birnin kasar ta Isra'ila, wanda zata gabatar a ranar 9 ga watan Yulin nan da zai kama, inda tayi Allah wadai da kisan Falasdinawa da Isra'ilan take yi.

DUBA WANNAN: Za a caji Ramos Pounds biliyan 1, saboda dukan Mohammed Salah da yayi

Kungiyoyi masu kokarin ganin sun share hawayen Falasdinawa, sun aikawa mashahuriyar mawakiyar da goron gayyata, don ta nuna rashin goyon bayanta ga Yahudawan Isra'ilan, inda nan take tayi maraba da goron gayyatar su.

Shakira mashahuriyar mawakiya ce wacce tayi kaurin suna a duniyar waka ta samu lambar yabo kala-kala ciki kuwa hadda wacce ta lashe a kwanan nan ta Grammy, haka zalika ita cebabbar jakadar bankin kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta bayyana cewa ta fasa yin shagalin wakar data shirya yi a kasar ta Isra'ila, inda kuma tayi Allah wadai da irin kisan gillar da Yahudawa suke yiwa al'ummar Falasdinu.

Sai dai kuma bisa dukkan alama matakin da mawakiyar ta dauka bai yiwa Yahudawan na Isra'ila dadi ba.

A yanzu haka dai kasar Isra'ila tayi kaurin suna wurin gallazawa al'ummar Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan gilla babu gaira babu dalili, musamman ma wadanda suke yankin zirin gaza, wanda a yanzu haka sojojin Isra'ilan suke zagaye da yankin.

A kwanan nan ne kasar ta Isra'ila ta kai wani mummunan hari kan Falasdinawan, inda ta kashe mutane da dama ciki kuwa hadda yara kanana.

To dai wannan ba shine lamari na farko da ya faru da kasar ta Isra'ila ba, al'ummar duniya dama kasashen duniya da dama suna yi mata kallon azzalumar kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel