‘Yan bindiga sun sace wani basarake a Jalingo bayan ya bar wurin murnar ranar dimokradiyya
- ‘Yan bindiga sun sace wani basarake mai daraja ta uku a garin Jalingo bayan ya bar wurin taron murnar ranar dimokradiyya
- Rahotanni sun bayyana cewar an sace basaraken ne tare da wani Dogarin sa da wasu mutane biyu a yammacin jiya
- Wata majiya daga cikin iyalin basaraken ta shaidawa jaridar Daily Trust cewar an sace Nuhu a garin Mutumbiyu dake kan hanyar zuwa Jalingo
‘Yan bindiga sun sace wani basarake mai daraja ta uku a garin Jalingo bayan ya bar wurin taron murnar ranar dimokradiyya. Basaraken, Abdulmudallabi Nuhu, shine sarkin garin Sansani a karamar hukumar Gassol.
Rahotanni sun bayyana cewar an sace basaraken ne tare da wani Dogarin sa da wasu mutane biyu a yammacin jiya, Talata, yayin da suke tafiya cikin motar basaraken. Har yanzu babu labarin inda basaraken da fadawan sa suke bayan sace su.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ba zai fadi zaben 2019 ba - Fadar shugaban kasa
Wata majiya daga cikin iyalin basaraken ta shaidawa jaridar Daily Trust cewar an sace Nuhu a garin Mutumbiyu dake kan hanyar zuwa Jalingo.
Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Taraba, David Misal, bai samu a waya ba, kasancewar wayoyin sa a kasha, domin jin tab akin hukumar ta ‘yan sanda.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng