Yanzu Yanzu: Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio zai ziyarci Buhari wata daya bayan zabarsa

Yanzu Yanzu: Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio zai ziyarci Buhari wata daya bayan zabarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio a yau Laraba 30 ga watan Mayu a fadar Aso Villa dake Abuja.

Legit.ng ta rahoto cewa Maada Bio zai ziyarci Najeriya wata daya bayan ya lashe zabe a matsayin shugaban kasar Saliyo.

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasar Saliyo a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu a Freetown, ta kaddamar da cewa Bio ya samu kuri’u 1,319,406 wanda yayi daidai da kaso 51.81 cikin 100 na kuri’un da aka jefa 2,546,577, inda ya kayar da dan takarar jam’iyya mai mulki.

Yanzu Yanzu: Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio zai ziyarci Buhari wata daya bayan zabarsa
Yanzu Yanzu: Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio zai ziyarci Buhari wata daya bayan zabarsa
Asali: Facebook

Bisa ga sakamakon, Kamara Wilson na jam’iyya mai mulki All Peoples Congress (APC) ya samu kuri’u 1,227,171 wanda yayi dai dai da kaso 48.19 cikin 100.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya yaba ma mutanen kasar Saliyo kan kammala zaben shugabancin kasa cikin nasara wanda aka gudanar a ranar 7 ga watan Mayu 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel