Kungiyar Arewa ta ba Buhari babban maki wajen tsaro da yaki da rashawa

Kungiyar Arewa ta ba Buhari babban maki wajen tsaro da yaki da rashawa

Kungiyar Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta gwamnati mai mulki babban maki wajen tsaro da kuma yaki da rashawa.

Kungiyar ta bayyana kalubale da kuma nasarorin da Najeriya ta fuskanta a shekaru uku da suka gabata a matsayin hanyar karfafa kasa.

A wata sanarwa daga babban sakataren kungiyar na kasa, Muhammad Ibrahim Biu, yace cigaba da ake wajen lugwigwita yan ta’addan Boko Haram, ceto sam da yan matan Chibok guda 100 da kuma yan matan Dapchi 104 da aka sace da kuma mayar da yan gudun hijira gidajensu ya nuna cewa lallai an duki mataki wajen dawo da zaman lafiya.

Kungiyar Arewa ta ba Buhari babban maki wajen tsaro da yaki da rashawa
Kungiyar Arewa ta ba Buhari babban maki wajen tsaro da yaki da rashawa
Asali: Depositphotos

"Hukumomin tsaro da na soji na magance matsalar rashin tsaro musamman rikicin makiyaya da manoma da kuma hare-haren barayin shanu a jihohin Nasarawa, Adamawa, Zamfara, Kaduna, Plateau, Taraba da sauran wuraren dake fama da wannan matsalar,” cewar kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Ba zan taba shiga harkar siyasa ba – Ali Nuhu

Kungiyar ta kuma bayyana cewa hukumomin dake yaki da rashawa na yin abunda ya kamata ta hanyar kama da gurfanar da barayin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel