Yadda wani malamin addini ya fitar wa da budurwa mai shekaru 39 kwankwaman da suka hana ta aure

Yadda wani malamin addini ya fitar wa da budurwa mai shekaru 39 kwankwaman da suka hana ta aure

Mun samu labari daga majiyar mu ta Daily Post yadda wani babban malamin addinin kirista a Najeriya ya tsulawa wata katuwar mata mai shekaru 39 a duniya da kuma take neman mijin aure ruwa-a-jallo domin ya fidda mata kwankwaman da ke hana ta aure.

Kamar dai yadda muka samu, matar mai suna Princess Josephine Uloma ta fito ne daga garin Orlu na jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya kuma ta fashe da kuka a majami'a yayin da take bayar da labarin yadda samun miji ya gagareta.

Yadda wani malamin addini ya fitar wa da budurwa mai shekaru 39 kwankwaman da suka hana ta aure
Yadda wani malamin addini ya fitar wa da budurwa mai shekaru 39 kwankwaman da suka hana ta aure

KU KARANTA: An soma korar karuwai daga Maiduguri

Legit.ng ta samu cewa matar dai tayi ta aman bayanai cikin shashshekar kuka na yadda ta kwankwaman dake kanta ke sa ta dukan dukkan namijin da yace yana son ta har dai suka gaji suka dena zuwa wurin ta.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Borno dake a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya a karkashin shugabancin Gwamna Kashim Shettima ta baiwa dukkan gidajen karuwai da na mashaya giya wa'adin kwana uku kacal domin su kwashe tarkacen su canja wuri.

Sanarwar hakan dai ta fito ne daga wani kwamitin din-din-din da gwamnatin ta kafa mai karfi karkashin shugabancin kwamishinan shari'a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan da mambobin sa na hukumar ma'aikatar filaye da safiyo na jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel