Ana zargin mawaki Kahutu Rarara da hutawa da kudin mawaka miliyan N100m
Ana zargin fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, da cinye wasu makudan kudade da yawan su ya kai miliyan N100m da aka bawa wasu mawakan arewa.
Rahotanni sun bayyana cewar gwamnatin jihar Zamfara ce ta bawa mawakan kudin saboda irin gudunmawar da suka bayar a yakin neman zaben Buhari a shekara 2015.
Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta na Facebook, Ibrahim Sanyi-Sanyi, ne ya fara kwarmata maganar bacewar kudin da gwamnatin jihar Zamfara ta bawa mawakan arewa ta hannun Rarara, amma kuma kudin suka yi batan dabo.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Haruna Aliyu Ningi, ne ya furta maganar yayin wata hira da manema labarai, kamar yadda Sanyi-Sanyi ya bayyana a shafin san a Facebook.
Mawakan, kamar yadda Ningi ya bayyana, sun ce zasu dauki matakan shari'a a kan Rarara domin ganin cewar bai cinye masu hakkin su ba.
DUBA WANNAN: Binciken wata kungiya ya gaskata furucin Buhari a kan 'yan Najeriya
Saidai, Ningi, bai bayyana ko sun shigar da korafin su wurin hukuma ba ko matsayar da suka cimma a kan maganar ba ya zuwa yanzu.
A shekarun baya ne dai Rarara ya taba rera wata waka mai taken "malam ya ci kudin makamai", wakar da wasu suka ce yana nufin tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, da ita. Sannan kafin nan ya taba rera wata waka, "masu gudu su gudu", dake nuna kyamar sa da cin hanci da kuma almundahana.
Ya zuwa yanzu dai majiyar mu bata samu jin ta bakin Rarara ba a kan wannan batu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng