Muhimman abbuwa 5 da Buhari ya fada a jawabin sa na yau

Muhimman abbuwa 5 da Buhari ya fada a jawabin sa na yau

Yau, Talata, 29 ga watan Mayu, 2018 aka yi murnar ranar tunawa da dawowa mulkin dimokradiyya a Najeriya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi mai tsawo ga mutanen Najeriya. Ga wasu muhimman abubuwa 7 daga cikin jawabin day a yi.

1. Matsalar tsaro: Daga cikin bayanin shugaba Buhari mai tsawon sakin layi 37 da suka yi Magana a kan abubuwa daban-daban, 9 daga ciki sun shafi sha’anin tsaro.

Shugaba Buhari ya yi bayanin irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu a bangaren tsaro da kuma irin matakan da take dauka domin shawo kan kalubalen tsaro da har yanzu kasar ke fuskanta.

2. Yaki da Cin hanci: Shugaba Buhari ya bayyana cewar abu na biyu mafi muhimmanci a gwamnatin sa shine batun yaki da cin hanci. Shugaban ya aike da sako ga ‘yan siyasa dake tunanin zai ajiye yaki da cin hanci saboda zaben 2019 na karatowa.

Muhimman abbuwa 5 da Buhari ya fada a jawabin sa na yau
Shugaba Buhari

3. Farfado da tattalin arziki: Ba iya bayanin yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya shugaba Buhari ya yi ba, ya yi bayani mai tsawo a kan irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu ta fuskar inganta tattalin arzikin Najeriya.

DUBA WANNAN: Yadda wasu matsaloli suka kusa raba ni da kujera ta - Gwamnan APC

4. Rawar da dattijan yankin Naija-Delta zasu taka a samar da zaman lafiya a yankin: Duk lokacin da aka yi maganar masu tayar da kayar baya a yankin Naija-Delta, shugaba Buhari kan sako batun rawar da dattijan yankin zasu taka domin samun zaman lafiya. A yau ma shugaba Buhari ya kara jaddada wannan kalami a cikin jawabin sa.

5. Maganar wutar lantarki: a kokarin sa na nuna irin kokarin da gwamnatin sa tayi a bangaren samar da wutar lantarki, shugaba Buhari ya bayyana cewar yanzu amfani da injinan samar da wuta (janerato) ya ragu a Najeriya. Kalamin da jama'a suka barke da cece-kuce a kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel