Yadda wata bakar guguwa ta lalata gidaje sama da 100 a jihar Kebbi

Yadda wata bakar guguwa ta lalata gidaje sama da 100 a jihar Kebbi

A ranar Lahadi ne da daddare wata mahaukaciyar iskar guguwa tayi matukar barna a garin Argungu na jihar Kebbi, inda fiye da gidaje 100 suka lalace.

Yadda wata bakar guguwa ta lalata gidaje 100 a jihar Kebbi
Yadda wata bakar guguwa ta lalata gidaje 100 a jihar Kebbi

Fiye da gidaje 100 ne wata mahaukaciyar iskar guguwa gami da ruwan sama mai karfin gaske suka lalata a garin Argungu na jihar Kebbi a arewacin Najeriya, a ranar Lahadin nan da daddare. Rufin kwanon gidaje da dama ya yaye ya zube kasa, ta yadda komai na cikin gidajen sai fito da su waje aka yi.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 16 da shugaba Buhari yayi magana akan su yau

Al'amarin ya sa mutane sun kwana a tsaye cirko-cirko a ranar da abun ya faru.

Wata mata Hauwa'u Muhammad da abun ya shafi gidanta ta shaida wa manema labarai cewa sun shiga tashin hankali su da yaransu, musamman yadda kura ta dinga turbude su.

Bayan komai ya lafa ne dai mutane suka yi ta aikin gayya don fara gyara muhallan nasu.

Tuni dai mutanen da lamarin ya shafa suka fara neman mafaka a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki, yayin da wasu kuma ke ci gaba da zama a gidajen, kasancewar ba su da wata mafaka.

A iya cewa al'ummar Argungu ba su taba ganin ibtila'i irin wannan ba.

Mataimakiyar Shugaban karamar hukumar ta Argungu Hindatu Umar Mai Zabo ta shedawa manema labarai cewa har yanzu suna tattara alkaluman mutanen da lamarin ya shafa, kafin a kai ga basu tallafi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: