Hukumar SSS ta sallami hadimin Kwankwaso, Yunusa Dangwani bayan watanni uku da yayi a tsare

Hukumar SSS ta sallami hadimin Kwankwaso, Yunusa Dangwani bayan watanni uku da yayi a tsare

- Hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya SSS, a ranar daren Litinin, ta saki jami’in Kwankwasiya, Yunusa Dangwani, bayan kwanaki 84 da ya share a tsare

- Mista Dangwani, tsohon shugaban ma’aikata na tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, an kamashi ne a ranar 21 ga watan Maris, a filin jirgi na malam Aminu Kano, a hanyarshi ta tafiya Umrah

- An kama Dangwani ne sakamakon sanya wani kaptin Abdullahi, ya tura sakon wayar salula, wanda suka hada da ‘yan uwan gwamnan

Hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya SSS, a ranar daren Litinin, ta saki jami’in Kwankwasiya, Yunusa Dangwani, bayan kwanaki 84 da ya share a tsare.

An kama Mista Dangwani, tsohon shugaban ma’aikata na tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ne a ranar 21 ga watan Maris, a filin jirgi na malam Aminu Kano, a hanyar shi ta tafiya Umrah.

Danwani, an kamashi ne sakamakon sanya wani kaptin Abdullahi, ya tura sakon wayar salula, wanda suka hada da ‘yan uwan gwamnan.

Majalisar wakilai a ranar 12 ga watan Afirilu, suka yanke hukuncin bincikar lamarin, na shiga hakkinsa da hukumar ‘yan sandan masu farin kaya sukayi game da tsare Dangwani, ya sabawa dokar kasa ta shekarar 1999.

KU KARANTA KUMA: Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega

Kotun tarayya dake zama a Apo, a ranar 3 ga watan Mayu, ta bayar da umurnin a saki Dangwani, sannan kuma hukumar ta SSS ta biyashi kudi N10m na shiga hakkinsa da tayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel