Buhari yayi alkawarin rattaba hannu akan dokar bawa matasa damar shiga siyasa
Shugaba kasa Muhammadu Buhari yayi alwashin amincewa da dokar nan da zata bawa matasa damar fitowa a dama dasu a siyasa wato "Not Too Young to Run" a turance
Shugaba kasa Muhammadu Buhari yayi alwashin amincewa da dokar nan da zata bawa matasa damar fitowa a dama dasu a siyasa wato "Not Too Young to Run" a turance. Shugaban kasar ya bayyana hakan a yau dinnan, a wurin bikin tunawa da ranar dimokradiyya da aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja.
DUBA WANNAN: Majalisar dattawa data wakilai suna kalubalantar Jega akan battancin da yayi akan su
"Nan da 'yan kwanaki kadan, zan rattaba hannu akan dokar da zata bawa matasan mu damar fitowa a dama dasu a siyasar kasar nan," inji shugaban kasar.
Sannan kuma ya bukaci dukkan 'yan Najeriya dasu so junan su da amana, sannan kuma suyi kokarin ganin sun zauna lafiya da juna. "Kamar yanda duka muke cikin murna zagayowar wannan ranar, muyi amfani da wannan dama mu so junan mu, sannan kuma dakatar da dukkanin wasu ayyuka na barna; daga hakane zamu samu irin cigaban da muke so a kasar nan," inji shugaban kasar.
Shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya dasu bada hadin kai da goyon baya, domin ganin an gabatar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.
"A karshe, nan da watanni kadan zamu shiga hada-hadar zabe. Ina so nayi amfani da wannan damar na tunasar da jama'a dasu bada hadin kai da goyon baya wurin ganin an gabatar da zaben nan cikin kwanciyar hankali da lumana, ta yanda za ake yin koyi damu a wasu kasashe na duniya," inji shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng