Da kyau: Jami'ar Najeriya 1 ta shiga jerin fitattun jami'o'in duniya

Da kyau: Jami'ar Najeriya 1 ta shiga jerin fitattun jami'o'in duniya

Jami'ar tarayyar dake garin Ibadan ita ce kadai jami'ar Najeriya da ta samu shiga cikin jerin jami'o'in duniya guda 1,000 da suka fi fice kamar dai yadda wata cibiya da ta shahara wajen bincike kan jami'o'in duniya mai suna Center for World University Rankings (CWUR) ta bayyana.

A cikin rahoton da cibiyar ta Center for World University Rankings (CWUR) ta fitar, ta lissafa jami'ar ta Najeriya a matsayin ta 991 a jerin jami'o'I 1000 na duniya sannan kuma ta 14 a Nahiyar Afrika.

Da kyau: Jami'ar Najeriya 1 ta shiga jerin fitattun jami'o'in duniya
Da kyau: Jami'ar Najeriya 1 ta shiga jerin fitattun jami'o'in duniya

KU KARANTA: Obasanjo ya fitar da rahoton binciken EFCC a kan sa

Legit.ng ta samu cewa babu dai wata jami'a daga Najeriya da ta samu shiga jerin na kwararrun jami'o'in na duniya bayan ita kuma.

A wani labarin kuma, Wani bakon haure daga yammacin Nahiyar Afrika mai suna Mamoudou Gassama ya samu daukaka a idon duniya da ma kasar Faransa ta Nahiyar turai bayan da ya sadaukar da ran sa ya ceto ran wani yaro mai shekara hudu a duniya daga halaka a birnin Paris.

Kamar yadda muka samu, bakon hauren da ya fito daga kasar Mali an ce ya nuna matukar bajinta lokacin da ya hau wani bene mai hawa hudu domin ya ceto ran wani jariri da ya ga zai fado ta tag.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng