Yadda Rahama Sadau ke yi idan zata ci tuwon Shinkafa da miyan kuka

Yadda Rahama Sadau ke yi idan zata ci tuwon Shinkafa da miyan kuka

Kanin jarumar dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Haruna ya bayyana cewa a duk lokacin da Rahma Sadau taga tuwon shinkafa da miyar kuka jikinta har rawa yake yi sai ta ga ta ci.

Haruna ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da jaridar Daily Trust bayan ya bayyana abincin da jarumar tafi so a matsayin Tuwon shinkafa da miyar kuka.

Yadda Rahama Sadau ke yi idan zata ci tuwon Shinkafa da miyan kuka
Yadda Rahama Sadau ke yi idan zata ci tuwon Shinkafa da miyan kuka

Yace a duk lokacin da ake girka wannan abinci toh zaka same ta tana sintiri daga madafa zuwa daki, idan kuma ya kasance ta fita aka girka toh idan ta dawo har rawa sai ta taka.

KU KARANTA KUMA: Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

Ya kuma jadadda cewa kowa a gida ya kwana da sanin cewa zata zamo mai nishadantarwa tunma kan ta zamo yar wasar Hausa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jarumar ta samu karramawa daga jaridar Leadership inda ta amshi lambar yabo a matsayin jarumar jarumai na shekara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng