Matsalolin APC ya fi na PDP da mukaita korafi a kai - Baraje
- Shugaban sabuwar jam’iyyar PDP na kungiyar cigaba, Alhaji kawu Baraje, a zantawar da yayi da Success Nogu, sun tattauna akan al’amuran da suka shafi bukatunsu daga jam’iyyar APC
- Kungiyar tayi korafi akan cewa ba’a kulawa dasu kuma ba’a sanyasu cikin al’amurran da ya kamata ace ana damawa dasu, sannan ba’a basu matsayin da ya kamata
- Kungiyar ta kuma bayyana cewa sub a wai sun bayar da wa’adi bane ga jam’iyyar game da hadasu da shugaban kasa, yace su shawara ce kawai suka bayar ko a cikin wasikar da suka rarraba
Shugaban sabuwar jam’iyyar PDP na kungiyar cigaba, Alhaji kawu Baraje, a zantawar da yayi da Success Nogu, sun tattauna akan al’amuran da suka shafi bukatunsu daga jam’iyyar APC.
Kungiyar tayi korafi akan cewa ba’a kulawa das u kuma ba’a sanyasu cikin al’amurran da ya kamata ace ana damawa dasu, sannan ba’a basu matsayin da ya kamata, misali kamar kujerar shugaban majalisa da muka nema.
Don haka suka ce matsalolin dake cikin gwamnati mai ci harma ya fi na baya da suke ta korafi a kai.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa su ba wai sun bayar da wa’adi bane ga jam’iyyar game da hada su da shugaban kasa, yace su shawara ce kawai suka bayar ko a cikin wasikar da suka rarraba.
KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai
"Muna fatan jam’iyyar APC zatayi abunda ya dace domin shugaba Muhammadu Buhari cigaba da kasancewa dan takararsu wanda kungiyar zata marawa baya.
"Duk da cewa ba’a girmama doka a wannan gwamnatin."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng