An kashe mutane 7 a wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara

An kashe mutane 7 a wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara

Hukumar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani sabon harin da 'yan bindiga dadi suka kai kauyen Gidan Labbo a gundumar Gidan Goga dake karamar hukumar Maradun dake jihar ta Zamfara

An kashe mutane 7 a wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara
An kashe mutane 7 a wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara

Hukumar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani sabon harin da 'yan bindiga dadi suka kai kauyen Gidan Labbo a gundumar Gidan Goga dake karamar hukumar Maradun dake jihar ta Zamfara. DUBA WANNAN: Duba kaga irin kudaden da gwamnatin tarayya ta samu cikin shekara daya dalilin wasu tsare-tsare data canja a kasar nan

Jami'in hulda da jama' a na hukumar 'yan sandan jihar, DSP Muhammad Shehu, ya bayyana faruwar hakan ga manema labarai a Gusau babban birnin jihar, a jiya Lahadi.

Yace 'yan ta'addan da har yanzu ba a kama su ba, sun kai hari kauyen Gidan Labbo a dajin Malikawa, inda far musu da harbi a dai-dai lokacin da suke gyare-gyaren gonakinsu don fara noman wannan shekarar.

"Muna samun rahoton, jami'an mu suka hanzarta tafiya kauyen, da zuwan su suka tarar da gawarwakin mutane 7."

Yace hukumar da sauran manyan cibiyoyin tsaro sun riga sun tura jami'an tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin.

Ya bukaci mutanen jihar da su cigaba da ba wa jami'an tsaro hadin kai da goyon baya ta hanyar basu bayanai akan 'yan ta'addan.

Majiyarmu Legit.ng ta ruwaito cewa: A jiya Gwamnan jihar Abdul'aziz Yari, ya bayyana cewa 'yan ta'addan suna ta aiko da sakonni na barazana ga manoman jihar, suna kuma umartar su da su bar gonakinsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin wani taro na raba takin zamani ga manoma na jihar a Nasarawar-Burkullu na karamar hukumar Bukkuyum.

Ya kwatanta tsoratarwar da abin tashin hankali ga mutanen jihar domin kuwa yawancin su manoma ne. Yayi alkawarin daukar kwakkwaran mataki ta hanyar samun shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin tsaro akan lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel