Boko Haram: Mutane 7 sun Mutu da yawa sun jikkata cikin lokaci kalilan a Borno

Boko Haram: Mutane 7 sun Mutu da yawa sun jikkata cikin lokaci kalilan a Borno

- Tsugunnu bai kare ba a jihar Maiduguri kan batun rikin Boko Haram

- A jiya ma wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar da Bam din jikinta da ya janyo Mutuwar Mutane uku

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) Bello Danbatta, ya tabbatar da cewa Bam din ya tashi ne a jiya Litinin kuma wata yarinya ‘yar kunar bakin wake ce ta tayar da shi a Mashamari dake Konduga, kusa babban birnin jihar ta Maiduguri.

Yar kunar bakin wake ta kashe Mutane 3 bayan ta da Bam a Borno
Yar kunar bakin wake ta kashe Mutane 3 bayan ta da Bam a Borno

Ya kuma kara da cewa “Mutane uku sun Mutu sanadiyyar harin yayinda bakwai kuma suka jikkata a harin da aka kai shi da yammacin jiyan.”

“Bam din da aka fara dana shi a Masallaci ya ta shi ne yayinda Mutane suke shirye-shiryen gabatar da sallah da yammaci jiyan kafin daga bisa dayan ya tashi a cikin gida.”

Haka zalika a yau ne Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar ta Borno Mr Damian Chukwu ya tabbatar da faruwar wani hari da ‘yan Boko Haram din suka kai garin Mashimari dake karamar hukumar Kondiga inda can ma Mutane hudu suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata bayan da suka harba wani abu mai fashewa a jiya.

Sai dai ya bayyana biyu daga cikin wadanda suka Mutum a matsayin farar hula, sannan ya cetuni sun kai jami’an tsaro wurin domin tabbatar da tsaro da kuma kwantar da hankula.

Idan ba’a manta ba a watan Fabarairun wannan shekara ne aka kashe Mutane 22 a wani mummunan harin Bam da aka kai kasuwar ‘yan kifi dake Kondugan wanda harin ya kasance daya daga ciki mafiya muni a tarihin garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng