Dubban mutane sun nemi a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

Dubban mutane sun nemi a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

Mutane na cigaba da nuna goyon baya ga wata takardar kara ta yanar gizo da ke neman a hukunta Sergio Ramos kan cewar ya ji wa Mohamed Salah ciwo da gangan.

An kai karar Sergio Ramos kan cewar da gangan ya yi wa Mo Salah keta a wasan karshe na gasar zakarun Turai da aka buga tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma ta Liverpool.

Majiyarmu ta wallaf cewa zuwa yanzu kimanin mutane 314,891 ne suka nuna goyon baya ga karar da ke neman a hukunta Ramos da aka wallafa a shafin koke na yanar gizo, petition.org.

Kawo yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, da ake naman ta hukunta Ramos ba ta ce komai game da karar ba.

Dubban mutane sun nemi a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah
Dubban mutane sun nemi a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

Ian dai bazaku manta ba tun ranar da lamarin ya faru ne dai Sergio Ramos ya yi wa Mohamed Salah fatan samun sauki da wuri.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ramos ya yi wa Salah fatan alkhairi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel