Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

- Wasu mata sun shiga hannun jami’an tsaro bayan an kama su dauke da jarirai guda biyu a binciken da jai’an Sojin Najeriya ke gudanarwa a Abaji, dake birnin tarayya

- Jami’an hana safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) sune suka fara bincikensu, da suka gaza bayar da kwakwaran bayani game da jariran suka zargesu, inda suka hadasu da jami’an sojin

- Matan bayan bincike mai kwari da aka gudanar a kansu sun bayyana cewa sun sato jariran ne daga asibitin jihar Abia, zasu kaiwa wani a Zuba, dake birnin tarayya

Wasu mata sun shiga hannun jami’an tsaro da jarirai guda biyu da aka kamasu dasu a binciken da jai’an Sojin Najeriya ke gudanarwa a Abaji, dake birnin tarayya.

Jami’an hana safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ne suka fara bincikensu, da suka gaza bayar da kwakwaran bayani game da jariran suka zargesu, inda suka hadasu da jami’an sojin, kamar yadda wani mai talla a wurin ya fadawa manema labarai.

Majiya daga hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa, matan bayan bincike da aka gudanar a kansu sun bayyana cewa sun sato jariran ne daga asibitin jihar Abia, zasu kaiwa wani a Zuba, dake birnin tarayya.

Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai
Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

Jami’in labarai ya samu labarin cewa an kai jariran gidan marayu dake birnin tarayya, kafin a gama gudanar da bincike saboda jami’an ‘yan sanda sunce bayyana matan ga mutane zai hana su gudanar da binciken da ya kamata su gudanar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shehu Sani ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Babban jami’in ‘yan sanda (DPO) na Abaji, Tersoo Tile, yace bai san da auwakuwar lamarin ba, lokacin da aka neme shi domin samun Karin bayani game da aukuwar lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng