Kasafin kudi: Wani ‘Dan Majalisa ya bayyana abin da ya sa aka kara Biliyan 500 cikin kasafin 2018
Honarabul Babangida Ibrahim wanda shi ne Shugaban Kwamitin harkokin kudi a Majalisar Wakilai ta Tarayya yayi hira da Jaridar Daily Trust kwanan nan inda yayi magana sosai kan kasafin kudin 2018.
‘Dan Majalisar da ke Wakiltar Yankin Kafur da Malumfashi yace bayan Shugaba Buhari ya gabatar da kundin kasafin na bana ne aka tafi hutun Kirismeti da sabuwar shekara. Sai dai kuma bayan an dawo hutun an gamu da wasu cikas dabam.
Daga cikin cikas din da aka samu shi Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati sun dauki dogon lokaci kafin su kare kasafin su a gaban Majalisa. Wannnan yana cikin abin da ya jawo aka bata lokaci kwarai inji Babangida Ibarahim.
KU KARANTA: Ni na gina Jami'o'i da Makarantun Almajirai a Najeriya – Tsohon Shugaba Jonathan
Honarabul Ibrahim yace Majalisar dai ta kara kasafin bana daga Tiriliyan 8.6 zuwa 9.1 ne saboda koke-koken da Ma’aikatu su ka rika kai wa cewa kudin da aka ware masu a bana yayi kadan. Irin su Hukumar NDDC dai su na cikin wannan sahu.
Bayan haka kuma babban ‘Dan Majalisar yace yana sa rai Gwamnati ta aiwatar da kaso mafi tsoka daga cikin abubuwan da aka yi niyya a bana saboda ganin cewa za a samu kudin da ake so domin kuwa man fetur ya kara kudi yanzu a Duniya.
Kun san cewa sai a kwanan nan ne Majalisa ta amince da kasafin kudin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban ta tun karshen bara. A kasafin bana Ma’aikatar ayyuka da gidaje da lantarki za ta samu sama da Naira Biliyan 680.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng