Duba kasar dake hana musulmai azumin watan Ramadana

Duba kasar dake hana musulmai azumin watan Ramadana

- Wata babbar kasa a duniya tana barazanar hana musulman cikin ta azumin watan ramadan, ko kuma su ajiye duk ayyukan gwamnati da suke yi, saboda tace baza ta yarda suna aiki suna azumi ba

- Ministar kasar tayi ikirarin cewar addinin musulunci bai yi kama da wayewar al'ummar wannan zamanin ba

- A shekarun baya dai kasar China ce dai ta taba yin irin wannan barazanar ga al'ummar musulman kasar, inda tace suma ko suyi aiki ko kuma su ajiye ayyukan su baki daya

Duba kasar dake hana musulmai azumin watan Ramadana
Duba kasar dake hana musulmai azumin watan Ramadana

A shekarun baya dai kasar China ta taba yin barazana ga al'ummar musulman kasar, inda tace ko suyi mata aiki ko kuma su je suyi azumin su. Domin sunfi bukatar ayyukan su fiye da azumin da suke, saboda azumi babu abinda zai karawa al'ummar kasar.

To a yau ma dai ministar shige da fice ta kasar Danmak, Inger Stojberg, wadda tayi kaurin suna sosai wajen kyamar masu neman mafaka wato 'yan gudun hijira, tayi barazanar ko Musulman dake aikin gwamnati a kasar ta Danmark su daina azumtar watan na Ramadana, ko kuma su ajje ayyukansu ga baki daya.

Ministar tace ta dauki wannan matakin ne saboda ma’aikatan kasar Musulmai masu yin azumin watan Ramadana zasu iya saka rayuwar al’umar kasar cikin hatsari babban.

Ga bayanin da ministar tayi:

DUBA WANNAN: Babu amfanin bikin ranar dimokradiyya a Najeriya - inji jam'iyyar PDP

“Ba zai yiwu ba mu damka tsaron dukiyoyin mu da kuma rayukanmu ga direban motar da ya wuni da yunwa bai ci abinci ba sannan ga kishin ruwa. Wannan ai debo ruwan dafa kai ne, ko kuma in ce banka wa kai wuta. Shi yasa, ko suyi wa kasar su aiki ko kuma suje suyi azumin su? su zabi daya! Hakazalika addinin musulunci da aka kafa shi akan dokokin al'ummar karnin baya, ba shi da wani wuri a harkar rayuwarmu ta yau da kullum. Saboda yana cin karo da yanayin wayewar rayuwarmu ”.

Amma sai dai hakan ya kawo kace-nace a kafafen yada labarai na duniya, inda wasu suke ganin kamar tauye wa musulman hakkin sune, tunda babu wata doka data hana mutum yin addinin sa.

To sai dai su dama gwamnatin kasar China tayi kaurin suna wurin nuna halin ko in kula a kan harkar addini. Wannan dai shine karo na farko da kasar ta Danmark ta fara yin barazanar ga musulman kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel