Yadda wasu matasa suka haƙo wata yarinya daga kabarinta suka datse mata kai a Adamawa

Yadda wasu matasa suka haƙo wata yarinya daga kabarinta suka datse mata kai a Adamawa

Rundunar Yansandan jihar Adamawa ta sanar da cafke wasu mutane uku dake da hannu cikin hako gawar wata karamar yarinya mai shekaru bakwai, tare da datse mata kai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Othman Abubakar ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu, inda yace lamarin ya faru ne a kauyen Tashan Baba dake kara hukumar Jada na jihar Adamawa.

KU KARANTA: Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa

Kaakaikin yace jami’ansu sun kama mutanen ne da kan wata yarinya mai suna Blessing Johnson, da suka sare mata kai, kwana daya da binne gawarta a makabarta, inda ya bayyana sunayen mutanen kamar haka: Yunusa Audi, Dauda Babale da kuma Muka’ilu Ishaya.

Dukkanin mutanen uku da Yansanda suka kama sun tabbatar da aikata laifin da ake zarginsu da aikatawa, inda suka ce wani mutumi mai suna John Bakari dake kauyen Karlahi ne ya basu kwangilar samo masa sabon kan mutum.

Yunusa, Dauda da Babale sun bayyana ma Yansanda a yayin bincike cewa wanda ya aiko su, John Bakari yayi alkawarin biyansu kudi naira miliyan biyar muddin suka sama masa sabon kan mutum, wannan ne ya sanya su hako gawar Blessing.

Sai dai kash! Kaakakin Yansanda ya tabbatar da cewa John Bakari ya tsere, amma suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kamo shi, kuma ya fuskanci sharia, ana sa ran gurfanar da mutanen uku a gaban Kotu ranar Litinin, 28 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel