Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa

Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa

A yayin da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ke farautar mutanen da suka yi watanda da kudin al’ummar kasar nan, su kuwa yayan jam’iyar adawa ta PDP kokawa suka yi dangane da yakin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan za’a tuna a satin da ya gabata ne dai hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon Ministan ilimi a zamanin Jonathan, Ibrahim Shekarau zuwa ofishinta dake Kano don gudanar da bincike akan naira miliyan 25 da take zarginsa da ci.

KU KARANTA: Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace

Daga bisan EFCC ta gurnafar da shi da tsohon shugaban yakin neman zaben Jonathan a zaben 2015 Aminu Wali kan tuhumarsu da kashe mu raba da naira miliyan 950 da aka basu kudin yi ma Jonathan yakin neman zabe.

Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa
Shekarau da Ramalan

Haka zalika a satin data gabata, EFCC ta maka tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang gaba Kotu kan badakalar naira biliyan 6.3, sai dai yayin da Shekarau ke ganin bita da kulli shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi masa, shi kuwa Jang cewa yayi ministan watsa labaru, Lai Muhammed ne ya sa aka kama shi.

Bugu da kari EFCC ta tasa keyar tsohon ministan ruwa, Mukhtar Shehu Shagari tare da kanin tsohon gwamnan Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa, Nasiru Bafarawa, gaban Kotu kan badakalar naira miliyan 500.

Shi ma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan sai da ya kwashe awanni hudu yana shan tambaya daga jami’an EFCC a Kaduna kan zargin wakaci wakatashi da suek zarginsa da yi da kudin zaben Jonathan naira miliyan 700. Kamar yadda EFCC ta shigar da dan takarar gwamnan jihar EDO a PDP Osagie Ize Iyamu, tsohon mataimakin gwamnan jihar, Lcuky Imaseun, da shugaban PDP a jihar kan badakalar naira miliyan 700.

Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa
Lamido da Jang

Baya da wadannan, shima tsohon Kaakakin PDP, Olisa Metuh, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, da na Katsina, Ibrahim Shema, da na Kebbi, Aliyu Dakingari duk suna fuskantar tuhume tuhume a Kotuna daban daban, haka zalika sunan shugaban PDP, Uche Secondus ya fito cikin jerin wadanda suka ci kudin makamai.

Sai dai Kaakakin jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta mayar da EFCC karan farauta, da take cuna ma yan adawa, shi kuwa ministan watsa labaru, Lai Muhammed cewa ya yi dole barayin PDP su dandana kudarsu sakamakon tatuke kasar nan da suka yi.

Fargabar da yayan jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu haka shi ne daga cikinsu wanene EFCC za ta damko wuyarsa anan gaba?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel