Ku daina zargin Buhari, ku tuba ga Allah – Ustaz Umar
Wani fitaccen malamin addinin Islama, Ustaz Umar Solomon, dake Abuja ya shawarci ‘yan Najeriya musamman matasa da su daina zargin shugaba Muhammadu ko gwamnatin bNajeriya a kan tsananin tattalin arziki da ake ciki a kasa tare da yin kiran das u fara gyara kura-kuran su tukunna.
Malamin ya bayar da wannan shawara ne yau, Lahadi, a Abuja yayin gabatar da wata lakca ta shekara da kungiyar “Afemai Islamic Movement (AIM) ta saba gudanarwa duk watan azumi.
Yayin gabatar da lakcar mai taken “yaki da cin hanci da kirkirar arziki a Musulunci”, Ustaz Umar y ace, “matsalar mu ba ta rashin manufar gwamnati ko rashin samun dama ba ne, matsalar mu ta rashin yin amfani da damar mu ne. Buhari ko gwamnati ba sune matsalar ba, babbar matsalar mu it ace ta rashin biyayya ga Allah da Manzon sa. Ba zamu taba ganin komai daidai ba saboda bamu dogara da Allah ba.”
DUBA WANNAN: Wata mai wurin sayar da abinci ta tsunduma cikin teku saboda an zarge ta da maita
Sannan ya kara da cewa, “Zama a gida tare da kin yin wata sana’a ko aiki ba shine dogaro ga Allah ba, saboda da yawan matasan da suka kamala karatu na zaune ne suna jiran gwamnati ta basu aiki ba tare da suna yin komai domin samun arziki ba.
Ya shawarci ‘yan Najeriya da su mayar da hankali wajen tunanin hanyoyin da zasu bi domin bunkasa hanyoyin yalwatar arzikin su tare da basu shawara a kan rage kasha kudi a kan abubuwa marasa muhimmanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng