Kocin Super Eagles, ya haramtawa 'yan wasan kwallon Najeriya soyayya da budurwansu, yayin wasan World Cup
- Rohr yaja kunnen wata yarinya cewa karta halarci sansanin Super Eagle a Russia
- Rohr yace mata da yaran wadanda zasu buga wasan ne kadai aka amincewa shiga wajen
- Ba abune mai sauki ba zabar mutane 25 daga kungiya
- Ba a amincewa yan wasa ganawa dako wace mace ba face matansu
Koch din Super Eagles Gernot Rohr yace a yayin wasan duniya da za'a buga a Russia ba a amincewa kowane dan wasa ganawa da wata ba face matansu da ya'yansu.
Ya bayyana haka ne a jiya yayin wani taro daya gudana a Uyo inda ya godewa gwamnan Akwa Ibom tare da masoyan su bisa ga goyan baya da suka basu.
A bangaren sa yace duk da cewa wasu daga cikin yan wasan basu da halin daukar nauyin matan nasu don kai musu ziyara a sansanin wasan, Captain Mikel Obi wanda yake auren wata yar Russian za'a bashi damar ganawa da matar tashi bayan gama wasan.
"Muma zamu bi sahun sauran kungiyoyin matayen yan wasa ne kadai da ya'yansu zasu samu damar ganawa dasu a ranar Lahadi bayan mun buga wasa ranar Asabar. Iyalan yan wasan suna da damar ganawa da mazajen su. Banda yan matan Russia da kuma na wasu guraren.
Zamu tsananta horo a lokacin da muke sansanin, ba a bawa duk wani dan wasa damar ganawa da wata mace ba face iyalin sa, zasu iya zama tare damu suci abinci idan sun so Sannan ko wane dan wasa yana da dakinsa iyalansa basu da matsala.
Rohr yace ba abune mai sauki ba zabar mutane 25 daga cikin kungiya wadanda zasu wakilci gasar ta kofin duniya.
DUBA WANNAN: Yajin aikin JOHESU ya kai intaha, kuma sunce yanzu suka fara
Yace idan mukayi wasa a matsayin kungiya daya zamu iya kaiwa zagaye na 16 wanda Daganan zamu kai matakin karshe, yakamata matasan su bamu goyon baya a Russia.
Obi yace "Ya kamata mu tuna cewa mu yan wasa ne na kungiyar kasa wanda zasu bada duk wani abu da suke dashi, Sannan inaso na kasance Captain na farko da zai lashe Kofin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng