Mata 'Yan Majalisa na kawo barazana ga Kujerar Osinbajo - Buhari

Mata 'Yan Majalisa na kawo barazana ga Kujerar Osinbajo - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa mata 'yan majalisun dokoki na jihohi dake fadin kasar nan cewa, su na kawo babbar barazana ga mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, matan sun bukaci a mayar da kujerar mataimakin shugaban kasa dindindin domin su kadai a kasar nan.

Jagoran na Najeriya ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin kungiyar mata 'yan majalisun dokoki na jihohin kasar nan da suka ziyarce a fadar sa ta Villa dake garin Abuja a ranar Juma'ar da ta gabata.

'Yan majalisun matan dai sun nemi shugaba Buhari ya zabi mace a matsayin abokiyar tafiyar sa wajen takara a babban zaben kasa na 2019 mai gabatowa.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, baya ga kujerar shugaban kasa, 'yan majalisun matan su na kuma bukatar shugaba Buhari ya zartar da doka ta cewar kowace jiha za ta sanya mace guda a kujerar majalisar dattawa cikin sanatocin da za ta fitar.

Doriya akan hakan, sun kuma bukaci mace 3 ta kasance cikin kowane 9 da jihohin kasar nan ke fitar wa a kujerar majalisar wakilai.

Mata 'Yan Majalisa na kawo barazana ga Kujerar Osinbajo - Buhari
Mata 'Yan Majalisa na kawo barazana ga Kujerar Osinbajo - Buhari

Legit.ng ta fahimci, shugabar wannan tawaga ta mata, Misis Elizabeth Ative, ita ta bayyana wannan bukatu ga shugaba Buhar a madadin 'yan uwanta mata 'yan majalisa, inda take cewa ana nunawa mata wariyar nau'in jinsi a siyasar kasar nan.

KARANTA KUMA: Taron Jam'iyyar APC: Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Adams Oshiomhole

A nasa martanin, shugaba Buhari cikin raha ya bayyana cewa, wannan bukata na kawo barazana ga mai rike da kujerar mataimakin shugaban kasa, watau Osinbajo.

Bugu da kari shugaba Buhari ya bayyana cewa kundin tsari mulki bai bashi dama ta tabbatar da bukatun su ba, inda ya ce mulkin soja ne kadai ke da ikon furta wannan bukatu da suka bayyana.

Dangane da furucin nuna wariya da ake yiwa mata a harkar siyasa cikin kasar nan, shugaba Buhari yace ko kadan ba gaskiya bane bisa la'akari da zabe mai gabatowa..

A karshe shugaba Buhari ya yi godiya ga 'yan majalisu dangane da goyon bayan sa, inda ya nemi su akan su ci gaba da dagewa akan hakan musamman a wannan lokaci da ya bayyana kudirin sa na sake neman takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel