Abun na yi ne: An sake sace sandar kungiyar majalisar tarayya
- Sandar girma ta kungiyar karamar majalisar birnin tarayya (AMAC) ta bata sannan an lalata wani banare na majalisar sakamakon rikici tsakanin ‘yan majalisar a ranar Alhamis
- AMAC tana daya daga cikin kananan majalisu shida dake akwai a babban birnin tarayya (FCT)
- Bacewar sandar ya kawo rikici sosai a cikin majalisar bayan kira da suka yi akan tsige shugaban majalisar Daniel Shanyibwa Michael, akan rashin adalci a jagorancinsa
Sandar girma ta kungiyar karamar majalisar birnin tarayya (AMAC) ta bata sannan an lalata wani banare na majalisar sakamakon rikici tsakanin ‘yan majalisar a ranar Alhamis.
AMAC tana daya daga cikin kananan majalisu shida dake akwai a babban birnin tarayya (FCT).
Bacewar sandar ya kawo rikici sosai a cikin majalisar bayan kira da suka yi akan tsige shugaban majalisar Daniel Shanyibwa Michael, akan rashin adalci a jagorancinsa.
Mataimakin shugaban majalisar Haruna Musa Saidu, yayi ikirarin cewa shugaban majalisar da saja mai daukar sandar ne suka dauki sandar suka gudu da ita daga majalisar.
KU KARANTA KUMA: Dandalin kannywood: Rahma Sadau ta samu lambar yabo a matsayin jarumar jarumai na shekara
Yusuf Tahir Kadir, shugaban masu rinjaye a majalisar shine wanda ya kawo shawarar tsige shugaban majalisar daga kujerarsa a zaman majalisar na jiya, sakamakon yana yanke hukunci ba tare da shawartar sauran ‘yan majalisar ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro suka gano sandar majalisar jihar Gombe wanda aka arce da ita a ranar Alhamis din.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng