Bayafara: Saura sati daya Najeriya ta balle - inji masu son kafa sabuwar kasa daga kudu

Bayafara: Saura sati daya Najeriya ta balle - inji masu son kafa sabuwar kasa daga kudu

- Tun 1966 ake son a balle Najeriya

- Dama dai auren dole ne aka daura wa kabilun Najeriya a 1914

- May 30 ce ranar tunawa da kafa Bayafara da kabilar Ibo ta taba yi

Bayafara: Saura sati daya Najeriya ta balle - inji masu son kafa sabuwar kasa daga kudu
Bayafara: Saura sati daya Najeriya ta balle - inji masu son kafa sabuwar kasa daga kudu

Maneman yancin Biafra sunce gwamnatin tarayya suna son hanasu abinda sukayi niyya na tabbatar da jamhuriyar Biafra a ranar 30 ga watan Mayu ta hanyar kawo jiragen yaqi a bangaren.

Sunce babu wasu jiragen yaki da za a kawo da zasu hanasu tabbatar da Biafra da kuma kwace gidan gwamnatin jihar Enugu, wanda zai zama hedkwata Biafra.

The Guardian ta gano cewa sojojin Najeriya da 'yan sanda suna ta lura da yankin ta jiragen sama tun ranar litinin, saboda tsoron tashin hankali da zai iya faruwa a yankin.

Shugaban BZF, Mani Benjamin Onwuka, ya sanar da manema labarai a Enugu cewa kungiyar ta shirya fuskantar duk wani makamin tabbatar da tsaro da zai iya barazana ga abinda sukayi niyya.

Yayi kira ga 'yan Biafra dasu jeru a gaban gidan gwamnatin jihar Enugu a ranar 30 ga watan Mayu. Inda yake umartar Gwamna Ifeanyi Ugwanyi da ya guji fitina ta hanyar tattara komatsan shi, da barin ofishin shi kafin ranar.

DUBA WANNAN: Ajje azumin 'yan kwallo, ya take ne

"Jiragen yakin da aka kawo yankin suna ta shawagi a jihar Enugu da kuma kudu maso gabas. Manufar su shine su saka mana tsoro. Amma muna so mu tabbatar musu, babu abinda zai tsorata mu. Wannan zamanin ya wuce. In har wani abu ya faru da daya daga cikinmu a wannan ranar, tabbas wadanda suke da hannu a ciki zasu yasa wa aya zaki."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng