Goron Azumi: Ku tsaya ku rika hutawa a yayin da gajiya ta cimmaku a wannan lokuta na Azumi - Hukumar FRSC ga Direbobi

Goron Azumi: Ku tsaya ku rika hutawa a yayin da gajiya ta cimmaku a wannan lokuta na Azumi - Hukumar FRSC ga Direbobi

Hukumar kula da manyan hanyoyi ta kasa watau FRSC (Federal Road Safety Corps), ta bayar da shawarwari ga direbobi akan su rika tsahirtawa su na samun hutu yayin da gajiya da kasala ta riske su a wannan lokuta na azumi.

Jami'in na hukumar ya bayyana cewa, ya kamata direbobi su rika dauka wasu lokuta kadan na samun hutu domin kiyaye afkuwa hadurra a yayin da gajiya da kasala ta cimma su musamman a lokacin azumi.

Mista Philip Ozonnandi, shugaban hukumar na reshen Ore, shine ya bayar da wannan shawarwari yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a garin Ore dake jihar Ondo.

Ozonnandi ya roki masu ababen hawa akan kiyaye dokokin hanyoyi, inda ya gargade su akan kada su ribaci wannan lokuta na azumi wajen yiwa dokokin hanya karen tsaye.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi Buda Baki da Shugabannin Majalisar Dokoki ta tarayya

Shugaban hukumar ya kuma gargadi direbobi da cewar watan azumi ba zai hana jami'an su sauke nauyin aiki da ya rataya a wuyansu saboda haka su tabbatar da kiyaye duk wata doka da hukumar ta gindaya.

Ya kara da cewa, ya kamata Musulmai su ribaci wannan lokuta na azumi wajen mika kokon su na bara ta hanyar kwarara addu'o'i na kiyaye afkuwar hadurra a kasar nan ta Najeriya da kuma neman zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng