Ka kawo karshen kashe-kashen da ake yi ko kayi murabus - Babban malamin addini zuwa ga Buhari

Ka kawo karshen kashe-kashen da ake yi ko kayi murabus - Babban malamin addini zuwa ga Buhari

Shehunnan malaman addinin kirista a Najeriya jiya sun bukaci shugaban kasar Najeriya da yayi murabus ko kuma ya tabbatar da samar da kyakkyawan tsaron da zai ba jama'ar kasar nan kariya daga kashe-kashe.

Babban Rabaran din Dakta Martin Uzoukwu da yayi magana a madadin sauran 'yan uwan sa yayin wani gangamin nuna rashin jin dadi game da kisan 'yan uwan su manyan malamai a jihar Benue ya bayyana cewa ba za su lamunci cigaba da kisan na su ba.

Ka kawo karshen kashe-kashen da ake yi ko kayi murabus - Babban malamin addini zuwa ga Buhari
Ka kawo karshen kashe-kashen da ake yi ko kayi murabus - Babban malamin addini zuwa ga Buhari

KU KARANTA: PDP ta zayyana halayyar wanda zata tsayar ya kada Buhari a 2019

Legit.ng dai ta samu cewa jiya ne dubun dubatar kiristocin kasar nan suka fita saman tituna a manyan biranen Najeriya suna masu zanga-zangar kisan su da suka ce ana yi a kasar nan.

A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Prince Uche Secondus ya shaidawa wakilin mu na kamfanin jaridar Punch cewa tuni shire-shiren hadewa da sauran jam'iyyun adawa a kasar nan domin kawar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019 yayi nisa.

Shugaba Secondus ya bayyana cewa kwamitin da jam'iyyar ta kafa karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas na samun gagarumar nasara don kuwa tuni sun kai wani mataki na fahimtar juna da wasu jam'iyyun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel