Mazari sarkin rawa: An dauki bidiyon wani Sanatan Najeriya yana cashewa da budurwa

Mazari sarkin rawa: An dauki bidiyon wani Sanatan Najeriya yana cashewa da budurwa

Kowa da kiwon da ya karbe shi, wai aka ce da manomin mai akuya ya sayo Kura, a iya cewa anan ma an sake kwatawa, inda wani zababbe da jama’ar sa suka zabe shi ya wakilcesu ya buge da tikar rawa.

Legit.ng ta ruwaito sanatan nan da ake yi masa lakabi da mazari sarkin rawa, Sanata Ademola Adeleke daga jihar Osun ya sake bajekolin basirar iya rawa dayake da shi, sai dai anan ba kamar yadda aka saba ganinsa yana rawar bane.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Majiyar mu ta dauko bidiyon Sanata Adeleke ne yayin dayake cashewa, yana barje gumi da wata tsaleliyar budurwa a wani wuri dake kama da gida, wanda hakan ya janyo cece kuce a tsakanin yan Najeriya.

Sai dai wannan ba zai zamo abin mamaki ba ga wadanda suka san halin Sanatan, kai asali me an ruwaito cewa kawu yake ga wannan shahararren mawakin nan dan Najeriya, Davido.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng