Shugaba Buhari na kokarin babbako da babban Kamfanin Najeriya Ajaokuta
Wannan Gwamnati ta Shugaba Buhari na kokarin yin abin da aka yi shekara da shekaru ba a iya yi ba a Najeriya kamar yadda mu ka samu labari daga Bloomberg. Gwamnatin Najeriya dai ta nuna cewa ba ta da kudin da za ta cigaba da narkawa a Kamfanin.
Kamar yadda mu ka samu labari, an sa rai Kamfanin na Ajaokuta na daf da fara aiki. Wani babban Jami’in Kamfanin Abdul-Akaba Sumaila ya bayyana cewa da zarar an dawo bakin aiki za a dauki Ma’aikata bayan an dade ba a kera ko kwai ba.
Kasar Rasha ce ta taimaka aka gina wannan makeken Kamfanin karafuna a cikin shekarun 1970s, sai dai bayan kashe sama da Dala Biliyan 8, har yanzu Kamfanin ya gagara fara aiki. Ana sa rai dai nan da wani ‘dan lokaci a soma kere-kere yanzu.
KU KARANTA: Ministocin da su ka fi samun kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2018
Gwamnatin Buhari ta ci buri kwarai a kan Kamfanin inda ta ke sa ran saida shi ga ‘Yan kasuwa. Hakan dai ba ai zo da sauki ba saboda sarkakiyar siyasa da tsarin aiki da kuma dokokin Kasar. Yanzu haka dai Kamfanin yana cikin wani halin ha’ulai.
Sai dai an dauko Abdul-Akaba Sumaila daga Kamfanin Royal Dutch Shell Plc domin ya dawo da Kamfanin na Ajaokuta bakin aiki kuma an kama hanyar hakan. Idan aka tada Kamfanin dinbin Jama’a za su samu aiki a Najeriya mai tarin jama’a.
Akwai dai gidajen Ma’aikata da dama a Kamfanin sai dai babu wani aikin da ake yi. Asali ma kuma Ministan Ma’adanan Kasar ya fito takarar Gwamna. Kuma Majalisar Tarayyar Kasar tace fau-fau ba za ta bari a saidawa ‘Yan kasuwa Kamfanin ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng