Sarkin Musulmi ya gudanar da rabon zakkar kudi N6m a jihar Sokoto
Kamar yadda kuka sani watan Ramadana yak an kasance lokaci na musamman ga al’umma Musulmi.
Sannan kuma lokaci ne da mutane kan ajirce wajen ibada da ayyukan alkhairi kamar su sadaka, kyauta da ciyar da mabukata.
Haka zalika akan fitar da zakka a baiwa talakawa da mabukata domin su samu damar yin ibada cikin walwala da farin ciki.
A yau Alhamis, 24 ga watan Mayu ne mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gudanar da rabon zakka da kudi da ya kai kimanin naira miliyan shiga ga talakawa a jihar Sokoto.
Ga hotunan rabon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa bata sanya hannu a kwamitin APC ba - Adesina


Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng