Birnin-Gwari: Yadda akayi ‘yan ta’adda suka kamani da wasu mutane 8 aka kuma sake mu - inji wani cikin wanda abun ya shafa
- Mutane tara da aka sace a karamar hukumar Birnin-Gwari dake jihar Kaduna, sun samu kubuta daga hannun wadanda suka sace su
- Daya daga cikin wadanda aka kama Lawali Ali, wanda aka fi sani da Mai bulawus Udawa, ya fadawa manema labarai cewa ba’a bawa ‘yan ta’addan ko sisi ba suka sakesu dan kansu
- Lawali yace wadanda suka sacesu din sun sanyasu yin tafiyar sa’o’I biyu cikin daji tare da wasu mutane 30 lokacin da suka sace su a safiyar Laraba
Mutane tara da aka sace a karamar hukumar Birnin-Gwari dake jihar Kaduna, sun samu kubuta daga hannun wadanda suka sace su.
Daya daga cikin wadanda aka kama Lawali Ali, wanda aka fi sani da Mai bulawus Udawa, ya fadawa manema labarai cewa ba’a bawa ‘yan ta’addan ko sisi ba suka sake su dan kansu.
Lawali yace wadanda suka sace su din sun sanyasu yin tafiyar sa’o’i biyu cikin daji tare da wasu mutane 30 lokacin da suka sace su a safiyar Laraba.
Lawali yace yana kan hanyarsa ta zuwa Kaduna a motar da ya shiga lokacin da aka tsayar da motar da ya shiga a Birnin-Gwari aka tsayar da ita a kauyen Labi.
KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Shugabar ma’aikata ta tarayya na kokarin kara albashin ma’aikata don inganta ayyukan gwamnati
Lawali mai bulawus ya bayyana cewa bayan ya fadawa ‘yan ta’addan cewa bashi da aikinyi kuma malami ne shi, sai suka raba shi da sauran mutanen, inda daga baya suka sallame shi tare da wasu mutane takwas a ciki hada wata mata wadda ke hanyar zuwa kauyen Wushishi a jihar Niger.
A halin da ake ciki, hanyar Birnin-Gwari ya zamo matattara ta yan fashi inda a kusan kullun akan samu lamari na garkuwa da mutane.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng