Dandazon al’ummar jihar Kano sun gabatar da sallar Al’kunut a kotu yayinda aka gurfanar da sardaunan Kano (hotuna)
A Yau Alhamis 24 ga watan Mayu ne aka gurfanar da kawo Malam Ibrahim Shekarau, sardaunan Kano a gaban babbar kotun tarayya dake Kano.
Dandazon jama'ar kano sun fito domin nuna bakin cikin su akan wannan lamari.
Kasancewar An jibge jami'an tsoro domin hana mutane shiga kallon shari'ar hakan yaba jama'a damar yin sallar al’kunut akan kwalta, sallar an gudanar da ita maza da mata harda wadanda ba yan jam'iyyar sa ba.
Zuwa yanzu a na gabatar da Shafi'u, sai dai abun jira a gani shine ko za'a bada su beli.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a gaban kotu bisa zargin raba mu kashe na kudi N950m na yakin zabe a 2015.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng