Gwamnan Gombe Dankwambo ya bayyana yadda ya samu sa’ar rayuwa ya kuma nemi a rika yi da Matasa

Gwamnan Gombe Dankwambo ya bayyana yadda ya samu sa’ar rayuwa ya kuma nemi a rika yi da Matasa

- Gwamnan Gombe ya nemi a rika cusa matasa cikin harkar mulki

- Gwamna ‘Dankwambo yace da haka ne dai Matasan za su san aiki

- Dr. ‘Dankwambo ya bayyana irin nasarar da ya taka a rayuwar sa

Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan ‘Dankwambo yana cikin masu bugun gangar a ba Matasa dama su shigo harkar siyasa a Najeriya. Gwamnan na Jam'iyyar PDP ya kara wannan kira a wannan makon.

Gwamnan Gombe Dankwambi ya bayyana yadda ya samu sa’ar rayuwa
Ibrahim Dankwambo ya nemi a rika damawa da Matasa

Gwamna Ibrahim ‘Dankwambo mai shekaru 56 a Duniya yayi kira a ba Matasa dama su taba mulki domin su fara samun kwarewa tun wuri. Gwamnan yace idan Matasan ba za su shiga fagen ba, ba za su taba gane dawar garin ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na cigaba da ciyar da 'Yan Makaranta

Ibrahim ‘Dankwambo yace ya fara hidimar kasa watau NYSC ne yana ‘Dan shekara 23 du-du-du a Duniya wanda bayan nan ya samu aiki a CBN yana ‘Dan shekara 35. Gwamnan ya karanci ilmin tattalin arziki ne a Jami’ar Legas.

Bugu-da-kari Gwamna Dankwambo yayi Digiri har na 3 watau PhD a wata Jami'ar Kasar nan wanda bayan ya bar babban Bankin Najeriya CBN aka nada shi a matsayin Akanta Janar na Jihar Gombe yana ‘Dan shekara 37 kacal a Duniya.

KU KARANTA: An ba Shugaba Buhari wa’adi ya sa hannu kan kudirin rage shekarun takara

Gwamnan duk yayi wannan bayani ne jiya a shafin sa na Tuwita. Gwamnan ya kara da cewa yana shekaru 43 da haihuwa aka nada shi Akanta Janar na kasa baki daya wanda bayan yayi shekaru a ofis din ya zama Gwamnan Gombe.

Kwanaki kun ji Dr. brahim Hassan Dankwambo yayi kira ga Matashin Mawaki Davido wanda yake tashe a Duniya cewa yayi amfani da basirar da Allah ya ba sa domin yayi kira ga Jama’a su karbi katin zabe mai zuwa domin kada kuri’ar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng